Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Kano ta kame wasu jami’an Hukumar kula da ababen hawa ta (KAROTA) bisa zarginsu da yiwa wani magidanci dukan kawo wuka, har ta kai ga sun karya shi.
Wannan rahoto ya fito ne daga Nasiru Salisu Zango, ma’aikacin gidan rediyo Freedom dake Kano a shafinsa na sada zumunta cewa kawo Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar CP Habu Sani ya umarci a mayar da binciken zuwa hedikwatar rundunar da ke Bompai.
Ya ce wata majiyar ‘yan sanda ta ce kame ‘yan Karotan ya fusata hukumarsu har ta janye jami’anta daga hanyoyin jihar Kano inda a baya suka saba gudanar da ayyukansu.
Sai dai kakakin hukumar ta KAROTA, ya musanta hakan, inda ya ce babu tabbacin cewar ‘yan karota ne suka aikata wannan mummunan aiki, sai dai bincike zai bayyana gaskiyar lamarin.
A nasa bangaren kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce ana kan bincike a kai.
A ‘yan kwanakin nan ana samun tangarda a yanayin tafiyar da aikin jami’an KAROTA a Kano, domin ko a makon jiya an zargi wani jami’in hukumar da galabaitar da wani matashi ta hanyar jona wa wata na’ura mai kashe jiki.
Da yawan mutane na kalubalantar hukumar ta KAROTA bisa yadda take wuce makadi da rawa a ayyukanta.
Wasu masana Shari’a na cewa hatta cin tarar kudi da KAROTA ke yi a yanzu ya saba da doka, domin kotu ce kadai ke da ikon cin tarar mutane idan sun yi laifi.
Maganar dokar hana goyon babur da KAROTA ta ayyana shi ma masana Shari’a sun bayyana shi a matsayin rashin dacewa.