Mai ɗakin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Aisha ta mayar da martani game da zanen barkwancin bikin ɗiyarta Hanan, wanda ya karaɗe shafukan sada zumunta tare da jawo surutai.
Zanen barkwancin na jaridar Daily Trust wanda Mustapha Bulama ya yi an nuna Aisha Buhari riƙe da hoton ɗaurin auren ɗiyarta ga ‘yan Najerriya suna nutsewa a cikin ruwa.
Kakakin Aisha Buhari, Barista Aliyu Abdullahi a yayin zantawarsa da sashen BBC kan batun ya ce ‘ya’yan
shugabanni na da ‘yancin yin aure idan lokaci ya yi ba sai jama’a na jin daɗin mulkin shugabanninba.
Zanen barkwancin na Mustapha Bulama da ke yawo bai yi adalci ba, domin ɗaurin aure ba ya cikin alamun nuna rashin damuwa da halin da ‘yan Najeriya ke ciki.
“Haƙiƙanin gaskiya, abubuwa irin waɗannan ne suka sa matar shugaban ƙasa ta gana da ma’aikatanta a watan jiya, inda ta shaida mana cewa tana so bikin ya kasance ba a tara jama’a ba, kuma babu babban biki.
Barista Aliyu ya ƙara da cewa, “hotunan ma’auratan da Aisha Buhari ta sanya a shafukan zumunta, ta sanya ne domin ta yi godiya ga masu fatan alheri, ba don ta ci mutucin ‘yan Najeriya ba.
“Zan iya cewa ɗaurin auren Hanan Buhari na daga ciki waɗanda aka fi yi ba tare da mutane sosai ba a Najeriya”.
Ya ƙara da cewa bidiyon da ke yawo na shagalin bikin ma’auratan inda ake musu liƙi da kuɗi a yayin da suke rawa, ba a fadar gwamnatin tarayya aka ɗauka ba, an yi ne a Kaduna, bayan an kai amaryar a gidan surukanta.
Ya ce uwargidar shugaban ƙasa na sane da ƙa’idojin kariya na cutar Koroma da aka sanya don haka ne ta tabbatar da dukkanin mahalarta sun kiyaye dokokin.
A ranar Juma’a 4 ga Satumba 2020 ne labarin bikin Hanan Buhari ya karaɗe shafukan sada zumunta, inda Aisha Buhari ta wallafa hoton ma’auratan.
Wasu sun yi ta ƙorafin cewa bikin ya zo a lokacin da ‘yan Najeriya ke fama da matsin tattalin arziƙi da kuma fama da annobar Korona.