Shugaban ƙasa Muhamamdu Buhari ya ce yawan ambaliya ruwan sama a jihar Kebbi na yin babbar barazana ga yunƙurin samar da wadataccen abinci a Najeriya.
Buhari ya jajanta kan ambaliyar da ta yi ajalin rayuka da dukiyoyi baya ga share dubban hektoci na amfanin gona, yana mai cewa lamarin ya jefa Najeriya a cikin barazana.
“Na damu matuƙa musamman game da wannan al’amari saboda ya kawo tangarɗa ga ƙoƙarin bunƙasa noman shinkafa domin hana shigowa da abinci daga ƙetare”.
Da yake ta’aziyya ga iyala mamatan, Buhari ya ce gwamantin tarayya za ta yi aiki tare da gwamnatin jihar Kebbi wajen tallafa wa waɗanda suka yi asara a sanadin ambaliyar.
https://dimokuradiyya.com.ng/yadda-ambaliyar-ruwa-ta-mamaye-kauyuka-40-a-adamawa/
“Mun mayar da hankali sosai a kan jihar Kebbi a shirinmu na samar da wadatacciyar shinkafa ‘yar gida da nufin farfaɗo da darajar noma da a baya aka yi watsi da ita.
“Asarar rayukan mutum shida da da dubbban hektoci gonakin shinkafa na sama da Naira biliyan ɗaya a jihar Kebbi, ya kawo babban cikas ga shirinmun na samar da abinci wadatacce.”
“Wannan abu ya yi muni sosai kasancewar manomansu da sauran ‘yan Najeriya na fatan samun amfani mai yawa a bana domin rage tsadar kayan abinci a kasuwanni”, inji sananrwar da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Mallam Garba Shehu ya fitar.