‘Yan sanda a Jihar Neja sun kama wani mai safarar makamai da bindigogi ƙirar AK-47 guda bakwai da albarusai guda 375 a garin Suleja na jihar Neja.
Mutumin ya ce shi ne yake dakon makamai ga wani gungun ’yan fashi da kuma garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.
“Ni direba ne, amma nakan taimaka wa masu wannan aikin wajen safarar makamansu domin samun ƙarin kuɗaɗen da za su taimaka min wajen kula da iyalaina.
“Nakan kai makaman ne ga wani Alhaji da ke zaune a Kaduna, amma wannan karon garin Keffi na Jihar Nasarawa zan kai kayan kafin a sami bacin rana a kama ni a Suleja”, inji wanda ake zargin.
https://dimokuradiyya.com.ng/yan-fashi-sun-hallaka-yan-acaba-biyu-a-kaduna/
Ya ce an biya shi N80,000 da ya kai kashin farko na makaman, an kuma yi masa alƙawarin N150,000 idan ya kai sauran wurin da ake buƙata, wanda daga ciki aka ba shi kafin alƙalamin N20,000.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, ASP Abiodun Wasiu ya ce jami’an sashen yaƙi da ‘yan fashi na SARS da ke kula da yankin Suleja ne suka cafke mutumin.
Ya ce an kama mutumin ne a wata mota kuma ya amsa cewa shi ɗan ƙungiyar ‘yan fashin ne da ya ƙware wajen yi musu safarar makamai.
Kakakin ya ce yanzu haka rundunar ta faɗaɗa bincike tare da yunƙurin ganin ta kama ragowar ’yan fashin.