Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa shirin ciyar da ɗalibai a yayin dokar kulle saboda cutar Korona ya laƙume sama da Miliyan 500, kamar yadda hakan ya fito daga bakin ministar agaji Sadiya Umar Farouk.
Ministar agajin ta bayyana cewa an aiwatar da shirin ne a jihohi guda uku a lokacin da aka rufe makarantu a watan Maris din shekarar da muke ciki.
Sadiya ta bayyana haka ne a yayin da kwamitin shugaban ƙasa kan cutar Korona ke karin bayani dagane da irin ci gaban da aka samu, kuma tace ba ma’aikatarta bace ta kirkiro shirin ba.
“Kafin mu fara aiwatar da shirin sai da shugaban ƙasa ya bada umarni, sannan muka tuntubi kungiyar gamayyar gwamnonin Najeriya, daga karshe muka samu matsaya akan cewa ciyar da yaran a gidajensu abu ne mai kyau.”
“Bayan cimma matsaya da muka yi da masu ruwa da tsaki an yarda akan a faro shirin daga birnin tarayya, jihar Legas da kuma Ogun a matsayin gwaji”.
Ministar ta ƙara da cewa sun yi amfami da ƙididdigar da babban bankin Najeriya wato (CBN) ya fitar na cewa kowame gida za a iya samun yara a ƙalla guda uku, kuma an tsayar da kashe naira 4,200 a matsayin kudin abinci na yara uku har tsawon wata guda.
Sadiya tace sun yi aiki da hukumomi daban-daban domin tabbatar da an yi aiki yadda ya kamata da kuma yin komai a fayyace.
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta ‘TrackNG’ ta bibiyi yadda ciyar da ɗaliban ta kasance inda tace 124,589 suka amfana da tallafin daga 14 ga watan Afrilu zuwa 6 fa watan Yulin shekara ta 2020.
A cewarta gidaje 29,609 ne suka amfana a Abuja, sai 37,589 a jihar Legas da kuma 60,391 daga jihar Ogun, wanda idan aka haɗa 4,200 tare da jumullar 124,589 zai bada adadin miliyan 523, 723, 800 na kudin da aka kashewa shirin.