‘Yan sanda a Najeriya sun saki Ibrahim Magu, dakataccen shugaban hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa, a cewar rahoton jaridar intanet ta Premium Times.
Jaridar ta ce an saki Magu ne a yammacin Laraba.
A makon da ya gabata ne ‘yan sanda suka tsare Ibrahim Magu kuma tun daga wannan lokaci ne wani kwamitin da Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa ya fara bincikarsa.
Gwamnati ta zargi Magu da gaza bayar da lissafin kuɗaɗen da hukumarsa ta yi iƙirarin ƙwatowa daga hannun waɗanda ta zarga da aikata cin hanci da rashawa.
“Kudi kimanin dalar Amurka biliyan 46 ne Ibrahim Magu ya ce an ƙwato amma biliyan 37 aka tarar a banki,” in ji Garba Shehu, mai magana da yawun Shugaba Buhari.