Gwamnatin Kasar Saudiyya ta sanar da cewa duk da annobar coronavirus, za a gudanar da aikin Hajji a bana a cikin wata mai zuwa, amma iya mazauna ƙasar ne kaɗai zasu samu damar gudanar da ibadar.
Kasar ta ce maniyyata ‘yan kadan ne za su samu halartar kuma mazauna wajen kasar ba za su samu gudanar da ibadar ba a wannan shekarar.
Ma’aikatar Kula da Harkokin Umarah da Aikin Hajji ta Saudiyya a cikin wata sanarwa a ranar Litinin ta ce ‘yan ko’ina a sassan duniya za su iya yin aikin Hajji, amma da sharadin ta kasance yanzu haka suna cikin kasar.
https://dimokuradiyya.com.ng/watakila-a-fasa-aikin-hajji-a-bana/
Hakan na nufin mazauna wasu kasashe, ciki har da ’yan asalin Saudiyya da ke kasashen ketare ba sa daga cikin wadanda za su yi babbar ibadar a wannan shekarar ke nan.
“Takaitaccen adadin mutane ‘yan kowace kasa da ke zaune cikin Saudiyya a yanzu haka za su iya yin aikin Hajji”, inji sanarwar, amma ba ta ambaci adadin alhazan da aka kayyade za su halarci ibadar ba.
Mahukuntan kasar sun dauki matakin ne saboda kare alhazai da sauran jama’a daga barazanar kamuwa da cutar coronavirus a lokacin aikin Hajji.