Kungiyar gwamnonin arewa maso gabashin Nijeriya, sun yi kira ga gwamnatin tarayya da za su karawa sojojin yankin kayayyakin aiki da zai ba su damar yaki da kungiyar Boko Haram a yankin.
Yankin sun bayyana hakan ne a cikin matsayar da suka fitar bayan zaman da suka gudanar a karo na biyu kan kalubalen da yake fuskantar yankin. Matsayar ta su wacce gwamnan jihar Borno, kuma shugaban kungiyar, Babagana Zulum.
Sun jinjinawa gwamnatin tarayya bisa yadda take yaki da ‘yan ta’adda, sai dai sun ce akwai bukatar jami’an sojin da suke yankin da su karfafa fadan da suke yi musamman a yankin da suke da wuyan shiga domin bai wa manoma damar zuwa gonakinsu su yi noma.
Sannan har wala yau sun nemi da a bai wa har wala yau ‘yan sanda damar yaki da Boko Haram din a inda ya dace, tare da samar da kayayyakin dakile ta’addanci da suka hada da; tiya gas, na’urar bibiya (trackers), muggan makamai da sauran su.
Har wala yau sun nemi da ma’aikatar ruwa ta gwamnatin tarayya da su tabbatar da sun sanya wa yankin Lake Chad ido wajen farfado da shi daga bushewa ta hanyar matatar ruwa ta kasa, tare da bunkasa kogunan da suke yankin.
Gwamnonin guda shida sun yi alkawarin aiki tare wajen ci gabantar da yankin, musamman wajen fito da danyen man fetur din da aka samo a yankin, da kuma sauran albarkatun kasa, noma da kiwo da kuma farfado da ma’aikatu.
Sannan sun yi kira ga gwamnatin tarayya da su kwace ayyukan titunan da ma’aikatar ayyuka suka bai wa ‘yan kwangila amma suka kwashe shekaru mai tsawon gaske har yanzu ba su kammala ba, domin bai wa wadansu ‘yan kwangilar da suka cancanta domin aikin. Sannan sun shawarci gwamnatin tarayya akan kammala aikin wutar lantarkin Mambila, da kuma sauran ayyukan da aka shimfida a karkashin hukumar ci gaban yankin arewa maso gabashi, NEDC da hadin guiwar gwamnatin jihohin.
Haka zalika kungiyar sun nuna goyon bayansu ga gwamnatin tarayya bisa manufofinta na yiwa tsarin almajirci garambawul domin bunkasa ilimin addini da na zamani tare da hana bara da a yankin kamar yadda gwamnonin arewa suka amince.
Kungiyar sun ayyana gwamna Zulum na Borno a matsayin shugaban kungiyar na tsawon shekara biyu, tare da ajiye Hedikwatar kungiyar a Maiduguri.
Gwamnonin da suka sami halartar wannan zaman sun hada da na; Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe.