Har wala yau Alhaji Mustapha Inuwa ya gargadi cewa cire dokar zaman gida da hana walwala da zirga-zirga a jihar, ba yana nufin babu cutar Korona ba ke nan a jihar. Inda ya ce har yanzu akwai cutar, wanda tsoffin mutane suka fi fuskantar hatsarin cutar, a don haka ya gargadi a guji shiga cunkuson jama’a tare da amfani da matakan kariya da bin shawarwarin Likitoci kan hana yaduwar cutar.
Wannan umurnin ya zo ne cikin takardar da Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Mustapha Inuwa ya rabawa manema labarai a ranar Alhamis a Katsina.
Inda gwamnatin ta tabbatar da cewa a bude kasuwannin daga 5 ga watan Yuni. Gwamnatin ta ce sun dauki wannan matakin ne bayan lura da yadda masu dauke da cutar Korona ke raguwa a jihar.
Kasuwannin dai da za a bude sun hada da; Charanchi, Mai’adua, Mashi, Dandume, Zango, Danja, Bakori, Yankara, Kafur da Dankama.
Sai kuma Kaita, Kagadama, Dutsi, Garkin-Daura da Kayawa, da sauran su.