A karon farko shugaba Buhari ya kare gwamnatinsa kan ƙarin farashin man fetur da wutar lantarki, wanda ’yan ƙasa musamman jam’iyyun adawa da masu sharhi suka yi ta suka.
Buhari ya ce tasirin annobar Korona ga tattalin arziƙin ƙasashe a faɗin duniya ce ta sa gwamnatinsa yin sauye-sauye ga manufofinta na dogon zango domin amfanin ’yan Najeriya, duk da cewa da farko ba za a ji daɗin hakan ba.
“Kuna sane da cewa farashin mai ya karye a lokacin dokar kulle a duniya, don haka muka cire hannu a farashin fetur domin masu saye su samu sauƙin farashi, wanda kowa ya yi na’am da shi.
“Abin da hakan ke nufi shi ne farashin zai riƙa sauyawa gwargwadon yadda kasuwar ɗanyen mai take a duniya.
Wato farashin zai ƙaru idan farashin ɗanyen ya samu tagomashi”, inji shi.
A jawabinsa ga taron bitar ayyukan gwamnatinsa a shekarar farko ranar Litinin, Buhari ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa duk da cewa babu tanadin tallafin mai a sabon kasafin 2020, gwamnati ba za ta kyale ’yan kasuwa su kara farashin mai barkatai ba.
Ta bakin Mataimakinsa Yemi Osibanjo, shugaban ya ce illar gwamnati ta ƙayyade farashin mai shi ne za ta biya tallafi, wanda ka iya jawo ƙarancin man.
“Yanzu kuɗaɗen shigarmu sun ragu da kashi 60%, don haka ba za mu iya biya ba.
“Na biyu shi ne yiwuwar dawowar dogayen layuka a gidajen mai, wanda ya zama tarihi a ƙarƙashin wannan gwamnti. ’Yan Najeriya ba sa wahalar bin dogayen layin sayen mai da yawanci aka yi wa ƙari fiye da ƙima.
“Sannan ba a yi wa tallafin mai tanadi a kasafin 2020 saboda ba za mu iya ba, idan har za a ba da kaso mai tsoka ga ɓangaren lafiya, ilimi da sauran buƙatu. Ba mu da zaɓi”, inji Osinbajo.
Ya ƙara da cewa, “yanzu aikin da ke gaban gwamnati shi ne hana ’yan kasuwa ƙara farashi barkatai da cutar ’yan ƙasa. Shi ya sa hukumar lura da farashin mai (PPPRA) a kwanakin baya ta sanya mizanin da gidajen mai ba za su wuce ba.
“Amfanin da aka samu yanzu shi ne kowa na iya kawo mai ya yi gasa da ’yan kasuwar, wanda hakan na iya sa su rage farashin”, inji Osinbajo.