Gwamatin Jihar Osun ta ce akwai yiwuwar ta dawo da dokar kulle biyo bayan kamuwar mutane 22 da cutar sarƙe numfashi a cikin awanni 24.
Kwamishinan Lafiyan Jihar Rafiu Isamotu, ya ce gwamnatin na duba yiwuwar sake rufe jihar sakamakon lamarin da ya faru washegarin ranar da wasu mutum 17 suka kamu.
“Ranar Alhamis mun sanar cewa mutane 17 sun kara kamuwa, abin takaici kuma mun kara samun mutane 22.
“Idan muka dubi abin da ya faru a baya, wannan babban abin damuwa ne kuma dole mu dauki mataki domin yaki da cutar Korona”.
Kwamishinan ya ce 11 daga cikin sabbin masu cutar an gano su daga cikin wadanda suka yi hulda da masu cutar ta COVID19 a yankin Ede da ke Osogbo, babban birnin jihar.
Da yake kokawa kan yadda jama’a ke yin burus da ka’idojin kariya, kwamishinan ya ce “Kwayar cutar na nan tare da mu. Dole mu bi matakan kariya, idan har muna so mu hana yaduwarta a cikin al’umma.
Ya ce zuwa yanzu, mutane 54 ne ke dauke da cutar daga cikin mutum 106 suka taba kamuwa a jihar, wadanda 47 daga cikinsu sun warke, wasu biyar kuma ta yi ajalinsu.