Mai karatu wannan ita ce cikakkiyar tattaunawar da wakilinmu Yahaya M Abdullahi ya yi da daya daga cikin Malamai a babban Jami’ar jihar Nasarawa dake Keffi, wato Dakta Idris Bashir Abdullahi wanda ya kasance daya daga cikin masu fashin baki na yau da kullum kan al’amuran siyasa da karatu a jihar Nasarawa. Wakilinmu ya zanta da shi ne bayan kammala jawabin da ya yi a dakin taro na Jami’ar NSUK bayan gudanar da gagarumin taro akan kare hakkin yara kanana wadanda ake yi musu fyade a fadin jihar Nasarawa dama kasa baki daya. Asha karatu lafiya.
Yanzu ana lokaci ne na take hakkin Yara mata ta hanyar yi musu Fyade, ko Ya ya Dakta yake kallon wannan lamarin?
Harkar Fyade wani abu ne wanda Malamai a makaranta da sauran manyan mutane a kasa sun yi rubutu akan fyade, wato shi fyade abu ne da ake yi da karfi kuma ba sai ga mace ba, a yanzu har namiji ana masa fyade amma abin da muke so mutane su gane shi ne, fyaden da ake yi yanzu ya canza kamanni ya zama wani abu daban, yanzu manya ne ke yi da kananun yara, Yara ‘yan wata biyu a duniya ko kuma ‘yan shekara uku a duniya za ka ga ana yi musu Fyade, to wannan magana na fyade dole mu zauna mu duba mu gani cewa, shin mene ne salsalar da yasa ake aikata wannan aika-aikar na fyade?
Wasu sun ce halin kulle ne da ake ciki wato ‘lockdown’ alhalin ba shi bane, idan rashin aiki ne zai sa ka yi fyade ai lokacin da ake aiki nan ma ana fyade, abin da zamu yi la’akari da shi shi ne, mu duba abubuwa makamancin haka, wadanda suka yi rubutu suna cewa abin da kesa fyade shi ne wanda ake musu fyade in ya zamanto ba a kula da su. Misali namiji ya ga yarinya karama kyakkyawa tana tafiya a cikin yanayi mai kyau tana ta yawo a Unguwa, ka ga wannan zai iya mata fyade saboda ya ganta a waje ba kula, amma idan tana cikin gida fa? Ya kamata mu duba wannan lamarin nan ma mu dunga killace yaranmu a gida ka da mu dunga barin su suna yawo ba tare da mun san ina suke zuwa ba.
Na biyu kuma abin da yake firgitar damu a wannan lokacin in ka duba ka ga irin kananan yaran da ake ma fyade, abin da za ka tambaya shin wadanda suke aikata wannan aikin na fyade shin ba su da hankali ne ko kuma wani ciwo ne na hauka yake so ya kama su? Abin da zamu duba mu gani, Ni a nawa tunanin, yanzu abun ya zama na hauka domin kuwa ya kamata mu dunga duba abubuwa biyu, na farko shi ne wanda na fada maka cewar rashin kulawa da yaran da ake musu wannan aikin, har yanzu hukumomi ba su hukunta wadanda aka kama su da wannan laifin ba, shiyasa wanda zai yi wannan aikin zai duba ai ba a hukunta wanda ya yi na baya ba ko kuma ai da na yi a baya ma ba a min wani hukunci ba saboda tunda babu wani hukunci to nima zanyi na ji ko kuma zan sake aikatawa in ya zamanto mai aikatawar ne, amma abin da muke so a yi la’akari da shi a nan shi ne, abu ne da ya kamata a ce ba wai kawai hukuma ne za ta yi ba, kowa yana da rawar da zai taka a wannan lokacin tun daga dan Sanda har kan Gwamna, ya kamata a zauna a duba idan ma za a yi doka ma masu aikata wannan mummunan aika-aikar ya kamata dokar ya zamanto tsakaninmu ne daga cikinmu.
Akwai wani Malami yana karantarwa a bangaren Shari’a ya ce in zaka yi magana akan hukunci zaka yi ne da yanayin jama’ar da kake tare da su, in ka yi dokar da bai shafi mutanen wajen ba ba zai yi tasiri ba. Kamar yanzu misali ka dauki dokar Keffi ka yi aiki da shi a Kano ba zai yi aiki ba, sai dai ka yi dokar Keffi da Keffi kawai, to ya kamata a duba wannan maganar na fyade, Iyaye su gaya ma yaransu ga matsalolin dake faruwa, wannan lamarin ya wuce maganan mutum ya yi domin ya ji dadi magana ne na wani abu daban wanda ba wanda ya sani sai wanda ya aikata hakan
Ko akwai wani Shawarar da Dakta zai bama Gwamnati kan masu aikata wannan aika-aikar?
Shawarata ga hukuma idan an kama masu irin wannan mummunan aika-aikar, kafin ma a zauna a ce an kaddamar da wannan dokar, ni shawarar da zan bayar shi ne kawai a yanke masa mazaqutarsa in dai in aka yanke zai rayu to kawai a yanke masa din, idan kuma ba zai rayu ba to a kashe shi kawai shi ne babban abin da za a yi domin maganin wannan mummunan aika-aikar.
Daga lokacin da aka kama shi ana kai shi to kawai a aikata masa wannan aikin na hukunci ko a kashe shi, ko kuma a yanke masa Mazaqutarsa kawai, ka da ma a saka masa bindiga, a yi amfani da bangaren rataya a rataye shi, a fito da shi kuma a fili gaban jama’a kowa na ganin irin hukuncin da ake yanke masa komai kudinsa kuwa, komai iyalansa, in ka duba sauran kasashen duniya za ka ga duniyar mutum bai hana a yi masa hukunci akan abin da ya aikata. Misali Amerika duk duniyar mutum in dai ya yi laifi to za su hukunta shi daidai da laifinsa, amma a kasarmu ta Nijeriya babu doka, ya kamata gwamnati ta yi la’akari da dukkan jami’ai tun daga Dan sanda har Hukumomi da ministoci ka da fa wannan sakacin ya sa mutane su fara daukar doka a hanunsu. Kamar Ni misali na yi karatun boko sosai, amma fa idan ka taba min yarinya fa ba ma doka, zan manta da doka ne kawai, ni da kai na zan dauki doka a hannuna matukar za ka taba min yarinya da sunan zaka aikata fyade da ita ko ka aikata.
Mun gode.
Dakta: Nima Nagode.