Rahotannin da ke shigowa jaridar Demokuradiyya yanzu na nuni da cewa, shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya amince zai sauka daga mulki kuma ya mikawa Joe Biden bayan majalisar dokoki ta rattaba hannu kan sakamakon zaben.
Amma duk da amincewa da mika mulki, Trump ya jaddada cewa lallai an yi masa magudi ne kuma shi ne sahihin wanda ya lashe zaben.
Ya jaddada cewa bai amince da sakamakon zabe ba, duk da cewa babu wata hujjar da ta nuna cewa an yi magudi.
Jawabin Donald Trump na cewa: “Duk da cewa sam ban amince da sakamakon zaben ba, kuma ina da hujjoji, zan mika mulki ranar 20 ga Junairu.”
KARANTA WANNAN: Yanzu yanzu: Shugaba Buhari ya shiga ganawa da wasu gwamnonin Arewa 2
“Tuni na lashi takobin cewa ba zamu yarda ba kuma sahihan kuri’u kadai za’a kirga.”
“Yayinda wannan ya kawo karshen mulkin shugaba mafi inganci a tarihi, yanzu muka fara yakin sake kara girman Amurka.”
Cikakken rahoton na zuwa…
A wani labarin, Rundunar ‘yan sanda ta gurfanar da wasu jami’an gwamnatin jihar Oyo a gaban kotun Majistire da ke Ibadan, bisa zarginsu da sata da sayar da buhuna 40 na sukari da aka kawo jihar da zummar rabawa jama’a a matsayin kayan tallafin COVID-19.
Wata yar kasuwa da ake zargin ta sayi kayan satar mai suna Kafayat Babalola ta gurfana gaban kotun tare da jami’an gwamnatin.
Jami’an gwamnatin da dan kasuwar ana tuhumar su da aikata laifin hadin kai, sata da kuma karbar kayan sata.
Wadanda ake zargin sun ne Adebiyi Azeez (50) da kuma Sunday Akinleye (43) wanda yana daga cikin jami’an da ke kula da alhakin raba kayan tallafin COVID-19 a ma’aikatar kananan hukumomi da masarautun jihar ne.
Jami’i mai shigar da kara, Sunday Ogunremi, ya shaidawa kotun cewa wadanda ake zargin sun aikata laifin ne a ranar 30 ga watan Disambar 2020.