Kungiyar shugabannin kasashen yammacin Afirka, ECOWAS sun bukaci da a soke zaben ‘yan majalisu 31 da ya tada hankali da ma jefa Mali a cikin rudani, sun dauki wannan matakin ne bayan taron da suka kammala.
Rahotanni sun nuna cewa; a cikin kwanaki goma da ke tafe dai, shugabannin kasashen na fatan cimma nasarar bukatarsu na ganin an kafa gwamnatin hadaka tare da ‘yan adawa domin wanzar da zaman lafiya a kasar ta Mali tare da kawo karshen tashin-tashinar da yake aukuwa.
Sanarwar bayan taron ta ambato cewar jerin matakan da kungiyar ta dauka wanda suka hada da soke zaben ‘yan majalisu 31 tare da sake sabon zabe, a wani abun da ke iya kai wa ga sanyaya zuciya ta kungiyar M5 din da ke fadin babu sahihanci a cikin zaben.