Wani mutum mai shekaru 61 da ya yi shekaru yana lalata da ‘yar cikinsa har ta kai ta ga daukar ciki, ya shiga hannun hukumar tsaro.
Tun yarinyar na ‘yar karama, mahaifin nata ya fara lalata ta, sannan ya ci gaba har ta kai shekaru 19 inda ta dauki juna biyu.
Yarinyar ta ce mahaifin nata da ya yi ta kwanciya da ita ba da son ranta ba ya yi barazanar yi mata dukan kawo wuka idan ta sake wani ya sani.
Ta ce bayan mahaifin nata ya gano ta dauki ciki sai ya kai ta wani kantin sayar da magani aka yi mata allurai aka kuma ba ta magani domin ta sha cikin ya zube.
Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Legas Bala Elkana, ya shaida wa manema cewa, hukumar tasu na bincike akan tsohon, yayin da aka kai yarinyar cibiyar kula da lafiya ta Mirabel domin a duba ta.
A wani ci gaban, Elkana ya kara da cewa wani mutum mai dan shekara 33 yana hannun rundunar bisa zargin sane da yin lalata da ‘yarsa mai shekaru 14.
“Wanda ake zargin ya amsa laifinsa, yanzu haka muna shirin gurfanar da shi a gaban kotu.
“Mun kai yarinyar mai shekaru 14 cibiyar kula da lafiya ta Mirabel domin ba ta kulawa”, inji shi.
Bala Elkana ya ce sun kame wadanda ake zargin ne duk a cikin watan Yuni. Wanda ya yi wa diyarsa ciki a unguwar Ikorodu, shi kuma na biyun a yankin Barga.