Matan ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Dass a jihar Bauchi Musa Baraza da ‘yarsa ɗaya da masu garkuwa suka sace sun shaki iskar ‘yanci.
A ranar Alhamis da ta gabata ne wasu da ba a san ko su wanene ba suka yiwa ɗan majalisar kisan gilla tare da tafiya da matansa biyu da ‘yarsa ɗaya a gidansa da ke ƙaramar hukumar Dass.
Matan ɗan majalisar sun haɗa da Rashida Musa Mante mai shekaru 40 da Rahina Musa Mante mai shekaru 35 sai kuma ‘yarsa Kausar Musa Mante mai shekara ɗaya a duniya.
Hakan na cikin sanarwar da shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar Bauchi Dakta Ladan Salihu ya wallafa a shafinsa na Twitter.
A cikin sanarwar ya bayyana cewa tuni gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammad ya baiwa likitoci da jami’an tsaro umarnin kula da iyalan gidan ɗan majalisar domin tabbatar da lafiyarsu.
Ko da wakilimu ya tuntubi kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Bauchi ta ya tabbatar da dawowar iyalan ɗan majalisar.