Hukumar ‘yan sanda reshen jihar Adamawa ta sanar da cewa tayi nasarar cafke wani shararren mai garukuwa da mutane, sannan sun kashe biyu daga cikin abokan mu’amalarsa, tattare da su an samu shanu 15, sai Tumaki guda 171 tare da harsashi mai yawan gaske da kuma bindigogi kirar hannu.
Hukumar ta sanar da hakan ne a ranar Juma’a ta hannun kakakin hukumar Mista Sulaiman Nguroje.
Nguroje yace wannan nasarar ta samu ne biyon bayan kiran kar ta kwana da suka samu daga wani mutum mai suna Yahaya Sale, mazaunin kauyen Ganji dake kamarar hukumar Gombi, inda ya shaidawa hukumar ‘yan sandan cewa wasu mutane da bai san ko su wane ba suna masa barazana da rayuwarsa.
Ya kara da cewa nan take suka tura jami’an kula da al’amarin da ya shafi yin garkuwa da Mutane domin yin bincike.
https://dimokuradiyya.com.ng/yadda-wasu-yan-bindiga-suka-yi-garkuwa-da-yan-uwan-juna-har-su-biyar/
Nguroje ya kara da cewa “ba jimawa da isar Jami’an sai masu garkuwar suka budewa jami’an wuta, nan aka dinga dauki ba dadi har muka samu nasarar kama shi babban cikinsu da kuma kashe wasu daga cikinsu, wasu kuma sun gudu cikin raunuka”.
Kamar yadda ya bayyana an samu dabbobi da kuma muggan makamai a tattare da su bayan kama shugaban nasu da aka yi.
Shugaban hukumar ‘yan jihar Olugbenga Adeyanju, ya tabbatarwa da jama’ar jihar cewa matukar yana jihar masu aikata muggan laifuka basu da mazauni kuma duk zai yi maganinsu.