Gwamnatin tarayya ta ce ta kwato fiye da naira biliyan 800 tare da gurfanar da fiye da mutum fiye da 1,400 a gaban kuliya a yakin da take yi da cin hanci da rashawa kamar yadda BBC Hausa ta labarto.
Ministan yada labaran kasar, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan a taron manema labarai a ranar Talata.
Ministan ya ce gwamnatin Shugaba Buhari ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin ta murkushe ayyukan masu cin hanci da karbar rashawa.
Lai ya ce: “Wannan gwamnatin za ta ci gaba da yaki da rashawa fiye da kowanne lokaci, kuma muna da alkaluman da suka tabbatar da hakan.”
“Wannan gwamnatin ta gurfanar da mutum fiye da 1,400 gaban kuliya ciki har da manyan mutane sannan ta kwato fiye da naira biliyan 800, ga kuma wasu attajirai da suka mika dukiyarsu,” in ji ministan.