Ministan harkokin wajen Nijeriya Geoffrey Onyeama ne ya maida kakkausan martani kan rushe mata ginin diflomasiyyarta a kasar Ghana.
Ministan ya bayyana hakan ne a shafinsa dake Twitter jim kadan bayan bayyanar batun rushe ginin Diflomasiyyar, ya ce wajibi ne Ghana ta dauki matakin kare lafiyar ‘yan Nijeriya da ke cikin kasar. Sannan ya nemi gwamnatin kasar Ghana ta yi karin bayani kan rushe gine-ginen.
Onyeama tuni gwamnatocin kasashen biyu suka fara tattaunawa kan batun wanda bayanai ke cewa an yi amfani da motar rusau wajen niqe gine-ginen Diflomasiyyar Nijeriyar.