Ministan matasa da ci gaban wasanni, Sunday Dare, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya cikin shekaru biyu masu zuwa za ta samarwa da matasa 200, 000 da ayyukan yi ta fuskancin horas da su a bangaren kimiyya wajen koya musu yadda za su hada shafukan Intanet, yin manhaja, da dai sauran su.
Minista Sunday Dare ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja, a yayin wani taron 2019 kan ‘Ranar Matasa Ta Afrika’ wanda aka yiwa taron take da; ‘Samar Da Miliyan Daya Zuwa 2021, Ku Sanya Ni Ciki.”
Ministan har wala yau ya ce; za a kuma koyar da matasan ayyukan AI (Artificial Intelligence), yadda ake samar da manhajar waya, gyaran wayoyin salula, tattara bayanai da kuma ‘coding.’
Ministan ya ce kungiyar Afrika ta zabi ta sadaukar da wata guda a shekararnan wajen gudanar da wannan taro mai muhimmanci. Sunday Dare ya ce za a samar da akalla matasa miliyan guda wadanda za su kasance cikin miliyoyin ‘yan Afrika wadanda za su amfana ta fuskancin ilimi, ayyukan yi, da kuma dogaro da kai wato 4Es a takaice.
Ya ce ranar 1 ga watan Nuwamba ita ce ranar matasa ‘yan Afrika, wanda shugabannin kasashe suka ayyana ranar a cikin watan Yunin 2006 da a birnin Banjul na kasar Gambiya.