Rahotanni sun ruwaito cewa rundunar ‘yan sandan ƙasar nan ta gayyaci tsohon mataimakin shugaban babban bankin Najeriya, Obadiah Mailafia zuwa ofishinta.
Rundunar ta buƙaci Mailafia da ya bayyana a ofishinta dake birnin tarayya Abuja a ranar Litinin.
Wannan sammacin na zuwa ne a lokacin da hukumar farin kaya ta DSS take bincikensa kan wasu zarge-zarge.
A cikin makon da ya gabata ne DSS ta gayyaci Mailafia da ya bayanna a ofishinta na Jos bayan da ya furta wasu kalamai a yayin wata hira da wani gidan rediyo inda ya zargi wani gwamnan Arewacin Najeriya da zama babban jigon Boko Haram.
A cewar wasu kafofin yaɗa labarai, wasiƙar wacce ‘yan sandan ta aikewa Mailafia mai ɗauke da sa hannun mataimakin kwamishina Umar Mamman Sanda ta bayyana cewa tana ƙara bincike ne kan zarge-zargen da ya yi.
Tuni dai hukumar da ke kula da kafofin watsa labarai ta ƙasa ta NBC ta ci tarar gidan rediyo na ‘Nigeria Info’ wacce ta gudanar da hirar tasa. NBC ta ce ‘Nigeria Info’ ya bayar da damar a wallafa labaran da za su iya kawo tashin hankali.
A yayin hirar Mailafia ya bayyana cewa ya samu labarin ne daga wasu tsoffin mayakan Boko Haram, amma daga baya a lokacin da ya ke bayar da haƙuri kan kalaman nasa ya ce “na san ya kamata in yi bincike kafin in yi magana saboda watakila an ba ni labarin boge.”