Gamayyar kungiyar #RevolutionNow tare da hadin gwuiwar kungiyar ‘Concern citizen’ ne suka afka komar jami’an tsaron Nijeriya da ya hada da soja da ‘yan sanda a babban birnin tarayya Abuja biyo bayan zanga-zangar da suka shirya gudanarwa a yau Laraba domin neman Nijeriya ta zauna lafiya da kuma yaki da rashawa da gurbataccen shugabanci kamar yadda suka bayyana.
Tun kwanaki uku da suka gabata ne dai kungiyar ta sanar da cewar tana nan zuwa domin gudanar da zanga-zangar lumanan kan halin da Nijeriya ke ciki da kuma yadda ake kashe mutane a kasar ba tare da wani dalili ba.
Sama da mutane 60 Jami’an tsaron suka kama a Abuja a yayin gudanar da zanga-zangar kamar yadda shugaban #RevolutionNow Omoyele Sowore ya tabbatar a shafinsa na Twitter.
Rahotanni sun nuna cewa baya ga haka kuma, sun katange dukkan wata mashiga a cikin garin domin masu zanga-zangar.