Ifeanyi Okowa ya sanar da cewa shi da mai ɗakinsa sun kamu da curtar, inda ya sanar da hakan a shafinsa na twitter.
“Ni da mai ɗakina mun kamu da COVID19 amma har yanzu da ƙwarinmu a inda muka killace kanmu”, ya wallafa.
Kamuwar gwamnan na zuwa ne kwana biyar bayan ya sanar da harbuwar ɗiyarsa wadda ta sa sauran iyalansa suka fara killace kansu.
https://dimokuradiyya.com.ng/gwamnan-jihar-ondo-ya-kamu-da-cutar-korona/
Okowa ya shiga sahun takwarorinsa gwamnoni da suka kamu da cutar ne washegarin ranar da Gwamnan Ondo Rotimi Akeredolu ya kamu da cutar.
A yanzu haka dai ya zama na shida a jerin gwamnonin da suka kamu da cutar ta sarƙe numfashi a faɗin Najeriya.