Gwamnatin tarayya ta ce babu ranar buɗe makarantu a ƙasar ko da yake tana kan tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin ganin an buɗe makarantun.
Minista a ma’aikatar Ilimi Nwachukwu Nwajiuba yayin jawabi a taron kwamitin yaƙi da Korona na ƙasa a Abuja ya buƙaci manyan makarantu da ke gunagunin ci gaba da rufe su da su ƙara haƙuri.
Ministan ya ce jami’o’i masu zaman kansu guda 78 sun bayyana wa gwamnati cewa a shirye suke su ci gaba da darussa amma manyan makarantun gwamnati ba su cimma matsaya ba.
Ya bayyana fatar nan ba da jimawa ba za a samu sanar da ranar buɗe makarantun, amma ba sasakai ba.
Ya ƙara da cewa Ministan Ilimi, Adamu Adamu da kansa ya tattauna da masu ruwa da tsaki na manyan makarantu game da batun na sake buɗe su.
Nwajiuba ya ce bayan sauraron dukkanin ɓangarorin da abun ya shafa, zai tuntunbi kwamitin yaki da cutar na ƙasa domin yin nazari kafin a kai ga ayyana ranar buɗe makarantun.