Sanata Buruji Kashamu mai wakilci Ogun ta gabas a majalisar datijjai daga shekara ta 2015 zuwa 2019 ya rasu sakamakon kamuwa da cutar Korona kamar yadda jaridar Punch ta wallafa.
Sanarwar ta fito ne daga shafin twitter na Sanata Ben Bruce a yammacin ranar Asabar.
“Abokina na kut-da-kut Sanata Buruji Kashamu ya rasu sakamakon COVID-19 a asibitin First Cardiology Consultants da ke Legas”, kamar yadda ya wallafa.
Ya kuma mika jajensa ga iyalan mamacin, wanda shi ne dan takarar gwamnan jam’iyyar PDP a jiharsa ta Ogun a zaben 2019.
https://dimokuradiyya.com.ng/da-dumi-dumi-surukin-ganduje-sanata-ajimobi-ya-rasu/
Marigayi Buruji babban jigon jam’iyyar PDP ne a yankin Kudu maso Yamma kuma tsohon shugaban kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar a yankin.
Shi ne kuma tsohon Mataimakin Shugaban Kwamitin Jihohi da Kananan Hukumomi a Majalisar Dattawa ta takwas.
A 2018 jam’iyyar ta taba koran shi kafin daga baya wata Babbar Kotun da ke zamanta a Abuja ta soke hukuncin a cikin shekarar.
Yanzu Buruji Kashamu wanda aka haifa a shekarar 1958, na daga cikin fitattun mutane a Najeriya da cutar COVID-19 ta yi ajalinsu tun bayan bullarta a watan Fabrairu.