Farashin man Amurka ya yi gagarumar faduwa a karon farko a tarihi. Hakan na nufin dillalan man fetur sai sun biya masu saye don su raba su da shi saboda ba su da wajen adana man sannan rufe rijiyoyin man abu ne da ake ganin akwai tsada.
BBC ta gano cewa matakin kasashe masu samar da danyen mai a kungiyar OPEC na rage yawan man da suke hakowa bai wani taka rawar gani ba na magance matsalar.
A jawabin da Shugaba Trump ya ke yi duk rana, ya ce Amurka za ta kara miliyan 75 na gangar mai ga ma’ajiyarta ta kasa.
Bukatar man a duniya ta ragu sosai saboda matakan kulle sun sa mutane na zaman gida