Gamayyar Majalisar wakilai ta kasa sun bayyana yardar su tare da amincewa da gyararren kasafin kudin shekarar 2020 inda ta kara shi daga N10.5 tiriliyan zuwa N10.8 tiriliyan.
Hakan ya faru ne duk da cewa kwamitin kula da kasafin kudin wanda rahotonsu aka yi amfani da shi a majalisar a ranar Laraba, sun bukaci a yi amfani da N10,801,544,664,642.
Sai dai ‘yan majalisar sun kara da naira biliyan hudu na walwalar kungiyar likitoci masu neman kwarewa bayan barazanar yajin aiki da suka yi.
Bugu da kari, majalisar ta amincewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aro kudi har dala biliyan 5.513 don amfanin kasar nan.