Majalisar dattawa ta musanta zargin karɓar ko sisin kobo daga Hukumar Raya Yankin Neja-Delta (NDDC) a matsayin tallafin rage raɗaɗin annobar Korona.
Majalisar ta mayar da martani ne ga Daraktan ayyuka na kwamitin riƙo na NDDC, Cairo Ojougboh, wanda yayin hira da manema labarai ya bayyana adadin kuɗin da ‘yan majalisun tarayya suka karɓa.
Dakta Cairo yayi iƙirarin cewa, kowane sanata ya karɓi naira miliyan 20 yayin da kowane ɗan majalisar wakilai ya karɓi naira miliyan 15 a matsayin tallafin rage raɗaɗin annobar Korona daga hukumar ta NDDC.
Sai dai cikin wata sanarwa da ta fito a ranar Talata daga kakakin majlasar dattawa, Sanata Ajibola Basiru, ta musanta zargin tare da ƙalubalantar Ojoughboh da ya ambaci sunayen ‘yan majalisar da aka bai wa kuɗin.
https://dimokuradiyya.com.ng/yan-siyasa-sun-maida-hukumar-nddc-naurar-atm-inji-akpabio/
Sanata Basiru ya ce: “majalisar dattawan ta fusata da wannan lamari da ba ɗauke a matsayin ƙarami ba, kuma ta ƙaryata cewa babu wani sanata da ya karɓi naira miliyan 20 ko wani kuɗi daga NDDC a matsayin tallafin Korona ko wani dalili na daban.
“Majalisar dattawan tana ƙalubalantar Dakta Ojougboh da ya fito ƙarara ya bayyana hujjar zargin da ya yi ta hanyar wallafa sunayen sanatocin da aka bai wa kuɗin.
“Muddin kuma ya gaza gabatar da wata hujja a kan hakan, majalisar dattawan na buƙatar ya janye maganar cikin gaggawa sannan ya nemi afuwar jama’a”, inji sanarwar.