Makarantu kuɗi a jihar Kano sun nemi gwamnatin jihar da ta yafe musu harajin zangon karatu na biyu saboda dokar kulle da ta shafi kowa da kowa.
Shugabar ƙungiyar masu makarantun kuɗi a jihar, Hajiya Maryam ta yi rokon ne saboda rashin biyan kuɗin makaranta da cutar Korona ta haifar.
Ta yi kiran ne bayan Gwamnatin Kano ta yi alkawarin tallafa wa malamai da sauran ma’aikatan makarantun kuɗi domin rage musu raɗaɗin halin da aka tsinci kai.
Gwamnatin Kano ta bayyana haka ne yayin rabon kayan kariyar lafiya (PPEs) ga makarantun gwamnati da masu zaman kansu 538 a faɗin jihar.
Tuni dai jihar ta fara feshin magani a makarantun da ke jihar a shirinta na buɗe su ga ɗaliban ajin ƙarshe na sakandare a ranar 10 ga Agusta.
Gwamna Abdullahi Ganduje ta bakin mataimakinsa Nasir Yusuf Gawuna yayin raba kayan ya ce masu makarantun kudi sun koka kan kalubalen da annobar COVID-19 ta kawo musu.
https://dimokuradiyya.com.ng/gwamnatin-jihar-kano-ta-ci-gaba-da-yin-rabon-kayan-tallafi/
Ya ce rabon kayan kariyar na daga cikin shirye-shiryen jihar na komawar daliban ‘ya ajin ƙarshe makarantun don fara jarabawa.
Ya buƙaci waɗanda suka samu tallafin su yi amfani da su yadda ya dace, su kuma bi ƙa’idojin da masana harkar lafiya suka shimfiɗa domin kawo karshen annobar.
Kayan da aka rarraba sun haɗa da takunkumai, sinadarin tsaftace hannu, kayan wanke hannu da kuma na’urar gwajin zafin jiki.
Kwamishinan Ilimi Sunusi Sa’id Kiru, ya ce daga cikin ɗalibai 27,454 da za su rubuta jarrabawar WAEC a jihar, kimanin 11,400 daga makarantun gwamnati suke yayin da 16,460 suke makarantun kuɗi.
Shi kuwa Kwamishinan Lafiya na jihar Dakta Kabiru Ibrahim Tsanyawa tabbaci ya bayar cewa za su tabbatar an tantance ɗaliban yadda ya kamata tare kuma da tabbatar da cewa suna wanke hannu akai-akai.