Mataimakin Gwamnan jihar Kwara kuma Shugaban kwamitin yaƙi da cutar Korona a jihar Mista Kayode Alabi tare da mai ɗakinsaAbieyuwa Alabi sun kamu da Korona kamar yadda sakamakon gwajin ya bayyana a ranar Litinin.
Mataimakin gwamnan tare da mai dakinsa sun fara bayyana alamun cutar wanda hakan ne yasa suka je aka musu gwaji, kuma sakamakon ya bayyana suna ɗauke da cutar.
https://dimokuradiyya.com.ng/korona-gwamnan-jihar-delta-ifeanyi-okowa-ya-kamu-da-korona/
Mataimakin gwamnan ya cika shekaru 57 a duniya a satin da ya gabata, kuma a baya an masa gwajin cutar wanda sakamakon ya bayyana bai kamu da cutar ba kafin daga bisani kuma ya kamu da cutar tare da mai ɗakinsa.
Gwamnatin jihar Kwara ta fitar da jawabi dangane da kamuwar mataimakin gwamnan shi da mai ɗakinsa, inda ta bayyana suna ci gaba da karbar kulawa kuma suna murmurewa kamar yadda ya kamata.