A jiya Alhamis ne wadansu matasa suka tare hanyar Dutsin Ma dake jihar Katsina a daidai garin Turare biyo bayan harin da ‘yan ta’adda suka kai kauyen Dogoruwa dake karamar hukumar Dutsin-Ma.
Wasu mazauna yankin sun shaida wa Majiyarmu cewa lamarin ya faru ne a kauyukan da Marke da Sanawa kuma Turare inda matasa suka rufe babbar hanyar Kankara zuwa Katsina.
Wani dan kato-da-gora da ke aiki a yankin ya shaida wa majiyarmu cewa kwanaki biyu da suka wuce ‘yan bidinga sun kai farmaki a kauyukan Kurecinge, Kurecin Malam da Marke da kuma Turare inda suka sace abin hannun mutane sannan suka tafi da wasu. A cewarsa, hakan ne ya fusata matasa suka fantsama kan tituna.
Rahotanni sun ce daga bisani an kai ‘yan sanda sun tarwatsa matasan.