A kalla mutane biyar ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya ritsa da su a kan titin Upper-Iweka dake babban birnin Onitsha a jihar Anambra.
Kamar yadda Jaridar Punch ta rawaito, da yawa daga cikin wanda hadarin ya ritsa da su sun ji rauni kuma an dauke su zuwa asibiti mafi kusa domin basu agajin gaggauwa.
Kakakin hukumar kiyaye hadura FRSC na jihar Pascal Anigbo ya tabbatarwa da Jaridar Punch faruwar hatsarin.
https://dimokuradiyya.com.ng/frsc-ta-daura-aniyar-ganin-takaita-hatsari-a-2020/
“Wani mummunan hadari ya faru akan titin Upper Iweka dake Onitsha, kuma mun tabbatar da rasuwar wasu mutane guda biyar a nan take”.
“A daidai wannan lokaci jami’an tsaro da suka hada da sojoji, ‘yan sanda, jami’an civil defense duk suna wajen domin bada taimakon gaggauwa”.
“A yanzu haka mutane biyar ne suka rasu amma da yake wasu suna ciki a makale ana kokarin ceto su, sannan sai muga mutane nawa ne suka rasu, nawa ne suka ji rauni”.