A kalla mutane 9 ne suka rasa rayukansu yayin da ‘yan fashi da makami suka shiga banki First Bank reshen Isanlu dake jigar Kogi.
Daga cikin wanda suka rasa rayukan nasu, sun hada da jami’an ‘yan sanda mutane takwas sai kuma farar hula mutum daya.
Daga cikin wanda aka kashe sun hada ‘yan sanda maza guda biyar da mata guda biyu.
An kashe shugaban caji-ofis na hukumar ‘yan sanda tare da mata biyu, sai kuma ‘yan sanda hudu, tare da guda daya da suka kashe a harabar bankin. Mutum daya na karshe ya rasu ne bayan da harsashi ya same shi a ciki.
https://dimokuradiyya.com.ng/kowa-ya-kwana-lafiya-jamian-tsaro-sun-cafke-wani-matashi-da-laifin-fashi-da-makami/
‘Yan fashin sun shiga caji-ofis da misalin karfe 1 na rana inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi, sannan sun saki dukkanin wanda suke daure a wannan caji-ofis.
Daga nan ‘Yan fashin suka garzaya banki, nan take suka kashe jami’in dan sanda guda kuma suka saci kudade masu yawa.
Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar ta Kogi William Ayah, ya tabbatarwa da Jaridar Punch faruwar lamarin, sai dai yace ana ci gaba da bincike domin tabbatar da adadin wanda suka rasu.