Gwamnatin jihar Legas ta bayyana cewa an salami mutum 32 da suka warke daga annobar cutar korona, inda ta ce cikin wadanda suka warke din, 27 ‘yan Nijeriya ne a yayin da mutum biyar kuma ‘yan kasashen waje ne.
Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar, shi ne ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi a garin Legas, inda ya ce wadanda suka warke an sallame su ne bayan gwajin ya nuna ba su dauke da cutar kuma.
“cikin mutum 32 wadanda suka warke, akwai mata 12, sai maza 20, ‘yan kasashen waje biyar, inda aka sallame su daga cibiyar killace masu cutar, inda suka koma cikin al’umma.” Inji shi.
Ya ci gaba da cewa; daga cikin wadanda suka warke sun fito ne daga Agidingbi; sai takwas daga Onikan; biyar daga asibitin dakile cututtuka masu yaduwa ta ‘Mainland Infectious Disease Hospital,’ Yaba; sai Tara daga Gbagada, hudu kuma daga ‘Vidic Centre’ sai biyar daga cibiyar killace masu cutar ta asibitin ‘LUTH.” Ya tabbatar.