Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce shi kadai ne ke da hurumin nadawa ko sauke wani Babban Hafsan soji a mukaminsa, sabanin umurnin da Majalisar Dattawan kasar ta bayar da ke cewa, hafsoshin sojin su sauka ko kuma a sauke su daga mukamansu.
Martanin wanda Kakakin shugaban kasa, Femi Adeshina ya sanyawa hannu ta ce, shugaban ya ji matsayin da Majalisar Dattawan ta dauka a wannan Talatar, amma su san da sanin cewar; “babu wanda yake da hurumin nada Hafsan soji ko kuma sauke shi daga mukaminsa sai shi (shugaban kasa) kadai,” ya tabbatar.
Ita dai Majalisar Dattawa a ranar Talata ne suka tafka muhawara kan tabarbarewar tsaro da kuma kashe sojojin Nijeriya da ‘yan bindiga suka yi a jihar Katsina, inda ‘yan majalisun suka nuna rashin amincewarsu da tabarbarewar al’amura a cikin kasar.
‘Yan Majalisun sun yanke hukuncin bai wa hafsoshin sojin shawarar sauka daga mukamansu saboda abin da suka kira “gazawa,” ko kuma a kore su daga bakin aiki.
Yan Nijeriya sun dade suna bayyana damuwa kan yadda harkokin tsaro ke tabarbarewa a kasarnan, lura da yadda ‘yan bindiga ke cin karensu babu babbaka a cikin kasar baya ga rikicin Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar.