Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo a yau Alhamis ya jagoranci zaman kwamitin tattalin arziki na kasa daga fadar shugaban kasa dake birnin tarayya Abuja. Inda zaman kwamitin ya wakana ta bidiyon Intanet.
Zaman ya gudana ne da dakin da ake ce ma ‘Yellow Room’ na ofishin mataimakin shugaban kasa, wanda wannan zaman shi ne irinsa na hudu a cikin shekara a daidai lokacin da Nijeriya ke yaki da annobar cutar Korona.
Ministar kudi tana daya daga cikin wadanda suka bayyana a zaman, a yayin da gwamnonin jihohi ma sun bayyana a zaman ta hanyar Bidiyo ta Intanet.
Shi dai kwamitin dai ya hada dukkanin gwamnonin jihohi 36, da gwamnan CBN, da ministar kudi, Sakataren gwamnatin tarayya da kuma wadansu kusoshi daga cikin jami’an gwamnati.