Jam’iyyar adawa ta PDP ta bukaci shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sauka daga shugaban Nijeriya sakamakon matsalar tsaro da yake ci gaba da addabar kasarnan. Tare da kuma yadda ake ci gaba da samun hauhawar cin hanci da rashawar a cikin gwamnatinsa.
PDP ta bayyana hakan ne a yayin taron manema labarai, inda ta jaddada cewa gwamnatin Buhari a rude take, ta inda ma ta rasa madafa balle makama. Har wala yau PDP ta nusasshe da cewa gwamnatin Buhari ta rasa abin da za ta saka a gaba wajen yaki da Boko Haram da kuma masu garkuwa da mutane tare da ‘yan bindigar da ke kashe-kashen jama’a ba ji ba gani.
Shugaban Jam’iyyar, Uche Secondus ya ce matsayin Majalisar Dattawa cewar hafsoshin tsaron Nijeriya su sauka daga mukamansu saboda gazawa wajen kare lafiyar jama’a, ya nuna cewar bangaren zartarwa ba ya aikin da ya rataya a wuyansa.