A Nijeriya, wasu mutane sun kai hari wanda ke nuna alama ce na ramuwar gayya a kan wuraren kasuwancin ‘yan Afirka ta kudu da ke birnin Ikko. Ba ya ga haka ma rahotanni da suke shigowa Jaridar Dimokuradiyya sun tabbatar da cewa; a yau Laraba ma wadansu fusatattun matasa sun kona ofishin MTN a garin Ibadan.
Sannan bayanai da dimi-diminsa da ke shigo mana a yayin hada wannan rahoton sun tabbatar da cewa; shagunan Shoprite dake birnin tarayya Abuja suna fuskantar hadarin, sakamakon yadda wadansu fusatattun matasa suka fuskanci wurin suna kone-kone.
Masu zanga-zangar a Abja sun nufi shagunan Shoprite dake titin zuwa filin jirgin sama, sai dai jami’an ‘yan sanda sun hana su isa ginin. Inda su kuma masu zanga-zangar suka fara kone-konen tayoyi da allunan talla.
Wannan lamarin ya haifar da cunkoson ababen hawa a titin zuwa filin jirgin saman, inda ya haifar da mutane suna ta juyawa.
Tun bayan da labarin kashe ‘yan Nijeriya ya ba zu a tsakanin ‘yan Nijeriya, ‘yan Nijeriya suka fara yiwa kamfanonin Afrika ta Kudu musamman shagunan Shoprite da MTN barazana.