Real Madrid za ta buga gasa uku cikin watan Janairu na shekarar 2021 da suka hada da La Liga da Spanish Super Cup da kuma Copa del Rey.
Real wadda take ta biyu a teburin L Liga ta shiga shekarar 2021 da kafar dama, bayan da ta doke Celta Vigo 2-0 a gasar Spaniya ranar 2 ga watan Janairu a filin wasa na Alfredo Di Stefano.
A watan na Janairu za ta fafata a karawa uku a La Liga, da daya a Spanish Super Cup wanda ta lashe a bara a Saudiyya da kuma fafatawa a Copa del Rey.
KARANTA WANNAN: Cutar COVID-19: Gwmana Fintiri ya haramta taron jama’a a jihar Adamawa
Ranar Asabar, Real za ta ziyarci Osasuna domin buga gasar La Liga karawar mako na 18.
Bayan wasan ne Madrid za ta kara a Spanish Super Cup da Athletic Bilbao ranar 14 ga watan Janairu.
Daga nan ne kuma kungiyar za ta fafata a Copa del Rey zagayen kungiyoyi 16 da suka rage a gasar, amma ba a bayyace wadda za ta fuskanci Real ba kawo yanzu.
Ranar 23 ga watan Janairu, Deportivo Alaves za ta karbi bakuncin Madrid a wasan mako na 19 a Gasar La Liga, kamar yadda jaridar BBC Hausa ta ruwaito.
Daga nan kungiyar da Zidane ke jan ragama za ta karɓi baƙuncin Levante a gasar La Liga ranar 31 ga watan Janairun.
A wani labarin, Hukumar da ke kula da katin shaidar zama dan kasa (NIMC), a ranar Laraba, ta sanar da cewa masu lambar dan kasa NIN za su biya N15,000 kafin a canja masu ranar haihuwa a rumbun ajiye bayanansu na hukumar.
A cewar ta, mamallakan lambar NIN za su biya N5,000 domin sabunta katin dan kasarsu ko kuma yin sabo idan wancan ya bace, da kuma biyan N500 idan za a canja adireshin da ke jikin lambar dan kasar.