Rundunar sojin ƙasar nan ta ce ta kashe ɗan fashi guda ɗaya tare da kama guda takwas a jihar Benuwe a ranar Lahadi.
Har wayau, rundunar ta kama guda huɗu da kuma karɓe makamai a hare-hare biyu da ta kai, a cewar wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na yanar-gizo.
Sanarwar ta ƙara da cewa dakarun rundunar Operation Whirl Stroke ne suka kai hare-haren a dajin Guma da ke kan iyakar jihohin Benuwe da Nassarawa bayan samun wasu rahotannin sirri cewa ‘yan fashin na zaune a dajin.
A wani simamen na daban, sojojin sun kama wasu mutane huɗu tare da bindigogi ƙirar AK-47 Gwer a jihar ta Benuwe, inda suka tarwatsa sansaninsu.