A jiya Litinin ne shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya gana da tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Adams Oshiomhole a fadar gwamnatin tarayya.
Shugaban ma’aikatan fadar Shugaban ƙasa, Farfesa Ibrahim Gambari, shi ne ya jagoranci zaman.
Wannan shi ne karo na farko da Oshiomhole ya ziyarci shugaba Muhammadu Buhari tun bayan da kwamitin gudanarwa na APC da aka ƙaddamar da kwamitin riƙo na jam’iyyar bayan rikicin jagoranci da ya ɓarke a jam’iyyar ta APC.
Oshimhole ya bai wa manema labarai tabbaci bayan ganawarsa da Shugaba Buhari cewa jam’iyyar APC ce za ta yi nasara a zaɓen da za a gudanar a jihar Edo, ya kuma ce ya nemi shugaban ƙasar ya samar da tsaro mai inganci a yayin zaben.
Ya kuma ce ya bukaci Shugaba Buhari ya tabbatar an gudanar da tsaftataccen zaɓe mai nagarta da kuma cikin lumana ta tsari na gaskiya da adalci.
Ya kuma nemi a hukunta duk wanda aka kama yana take doka, ko tayar da zaune tsaye ba tare da la’akari da jam’iyyar da yake goyon baya ba.