Shugabannin yankin Arewa ta tsakiya a Najeriya sun buƙaci shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya kori manyan hafsoshin tsaro saboda gazawarsu wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro.
Gamayyyar dattawan yankin ƙarƙashin inuwar (CNCE) ta ce kiran ya zama dole saboda rahoton hukumar Kwastam da ke cewa mayaƙan Boko Haram sun yi sansanonin a yankin da nufi kai hare-hare hare a Abuja.
“Muna baƙin cikin cewa babu jihar Arewa ta tsakiya da ba ta fama da hare-haren ‘yan ta’adda ko kashe-kashe, alhalin a bayan an san yankin da zaman lumana,” inji ƙungiyar.
Shugaban CNCE Usman Bida da sakatarensa Moses Okudu sun ce rahoton hukumar Kwastam “shi ne irinsa na farko a tarihin Najeriya” sakamakon gazawar “tara bayanai” daga hukumomin tsaro.
CNCE ta ce rahoton hukumar Kwastam na taruwar ‘yan Boko Haram a Abuja ya isa zama hujja a kan gazawar shugabancin tsaron da ke buƙatar a fara da sallamar manyan hafsohi kafin komai.
https://dimokuradiyya.com.ng/ni-kadai-ke-da-ikon-sauya-hafsoshin-tsaron-nijeriya/
Sanarwar na zuwa ne bayan Rundunar Tsaro ta Najeriya ta sanar da cewa ta riga ta sha gaban masu niyyar kai harin.
Sanarwar da kakakin runduanr tsaro, Manjo Janar John Enenche ta fitar a ranar Lahadi ta ce dakarun soji a tsaye suke domin daƙile duk wata barazana, ya kuma buƙaci mazauna da su kwantar da hankalinsu su ci gaba da harkokinsu.
Wannan dai ba shi ne karon farko da aka sha yin kira da shugaba Buhari ya tisa ƙeyar manyan hafsoshin ba, saboda zarginsu da gazawa.
A baya shi da kansa ya yi musu kashedi inda ya ce ƙoƙarin da suke yi bai wadatar ba wajen samar da tsaro a ƙasar nan, mai fama da hare-haren Boko Haram da barayin shanu da masu garkuwa da mutane da ‘ya fashin daji da rikicin manoma da makiyaya da na ƙabilanci da masu tayar a ƙayar baya.