SIYASA: Ba abinda Buhari yazo yi face Sata, Kisa da kuma tarwatsa Najeriya – Fani Kayode.
Tsohon Ministan Femi Fani Kayode ya bayyana shekaru biyar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a matsayin ‘Annoba’.
Ya kalubalanci mai bawa shugaban kasa shawara akan kafar yada labarai Mista Femi Adesina na cewa Buhari ya ceci kasar nan daga neman durkushewa a shekara ta 2015.
Kayode ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa zaman Buhari shugaban kasa ba abinda ya haifar face tsanani.
Kai tsaye ya mayarwa da Femi Adesina martani akan jawabin da ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa zuwa Buhari ba komai ya kara ba sai bakar wahala, duhu, da kuma tarwatsa komai.
“A cikin shekaru biyar da yayi ba abinda ya tsinana face sata, kisa da da lalata komai”.