A ci gaba da fatattakar ɓata gari a Arewacin Najeriya, musamman yankin Katsina, Zamfara da jihar Sokoto, sojoji sun harbe ’yan binidga 100 tare da tsare guda 148 tare da kwato mutane 107 a hannunsu.
Rundunar dakarun tsaro ta Operation Sahel Sanity a yankin ta ce ta ƙwace bindigogi 143 da harsasai 3,261 daga ’yan bindigar waɗanda aka kama shida daga cikin masu yi musu fasa-ƙwaurin makamai.
Kakakin rundunar, Birgediya Benard Onyeuko, ya ce masu yi wa ’yan fashi daji leken asiri 20 da masu yi musu safarar abinci 32 sun shiga hannu.
A jawabinsa a babban sansanin Soji da ke Faskari, Jihar Katsina babban hafsan ya ce sojojin sun cafke mutum 13 da ke sayar da shanun sata a jihar da masu hakar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba guda 315 ɗauke da harmtattun makamai a Jihar Zamfara.
https://dimokuradiyya.com.ng/sojoji-a-jihar-zamfara-sun-yi-nasarar-cafke-yan-bindiga-50/
Rundunar ta ce ta ƙwato shanu 3,884 da Tumaki 1,627 daga hannun ɓarayin daji a jihohin Katsina da Kebbi da Sokoto da kuma Zamafara.
Sun kuma tarwatsa sansanoni 81 na ‘yan fashin daji ciki har da maɓoyar hatsabibin ɗan fashin daji da ake kira Dangote a Jihar Katsina.
Ya ce dakarun suka daƙile hare-hare ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane guda 128 a yankin.