Hukumar ‘yan sanda reshen jihar Legas ta bayyana cewa ta yi nasarar cafke wasu ‘yan kungiyar asiri, a tare da su an samu bindigogi kirar hannu, da kuma sauran muggan makamai a tattare da su.
Hukumar ta ce sun samu nasarar cafke ne a yayin da suke gabatar da taron da suka a saba a wani gini da ba a kammala shi ba. Masu laifin dama sun addabi yankin Ikorodu na jihar da aika muggan laifuka.
Daya daga cikin wanda suka shiga hannun hukumar mai suna Gbadamosi Mohammed, yana daga cikin wanda ake zargi da kashe Madariola Sunday a watan da ya gabata.
https://dimokuradiyya.com.ng/dan-shekara-16-da-ya-kashe-yaro-a-legas/
Daga cikin wanda aka kama din sun amsa cewa su ‘ya’yan kungiyar Eiye, Aiye, KK, Buccaneers ne.
Kakakin hukumar’yan sandan jihar ta Legas DSP Elkana Bala, ya tabbatar da nasarar cafke masu laifin kuma yace hukumar tana ci gaba da bincike akansu kafin ta tura su kotu domin yanke musu hukunci.