Jagoran jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya nemi tsohon Shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar da ya yi hakuri ya koma jam’iyyar APC.
Tinubu ya ce, ko ba komi hakan zai ba Atikun dama wurin taimakawa a gina kasa tare da shi.
Tinubu ya fadi hakan ne a wata takardar sanarwa da ya fitar kuma ya rattabawa hannu, bayan hukuncin da kotin daga ke sai Allah Ya isa ta yanke dangane da daukaka karar da Atikun ya yi kan zaben Shugaban Kasa da ya gabata.
A cikin takardar sanarwar, Tinubu ya taya Buhari da jam’iyyarsu ta APC murnar wannan nasara. Sannan kuma ya yi kira ga Atiku da ya shigo cikinsu don a tafi tare a ceto kasa.