Jami’an hukumar kiyaye haɗura har mutane 3 sun rasa rayukansu sakamakon tsawa a jihar Ogun.
Jami’an da tsautsayin ya rutsa da su suna bakin aiki ne lokacin da lamarin ya ritsa su a ranar Laraba a karamar hukumar Ijebu-North East.
Mai magana da yawun hukumar a jihar ta Ogun, Florence Okpe, ta tabbatar da faruwar lamarin.
Lamarin dai ya auku ne a lokacin da jami’an ke cikin ofishinsu da ke yankin a daidai lokacin da suke shirin fitowa fareti da misalin karfe 10 na safe.
A lokacin da lamarin ya auku dai jami’an da ke wajen sun haura goma.
Ta ce “an sanar da hukumar mu faruwar lamarin, kuma shugabanmu ya tafi can dan ganewa idonsa, a yanzu ba zan iya bada hakikanin abinda ya faru ba, sai dai idan mun ji ta bakinsa”. Cewar Okpe.