Wani mutum mai shekaru shekaru 40 a duniya mai suna Lanre Kazeem ya kashe kansa ta hanyar rataya da safiyar ranar Lahadi a gidansa dake Eyin Grammer area a Ibadan.
Rahotanni sun bayyana cewa Marigayin yana rayuwa ne a gidan haya, kuma yana aiki ne da wani kamfani mai zaman kansa mai suna palm kernel company dake Soka Ibadan.
Al’ummar dake yankin sun yi matukar kaduwa bisa wannan abin da ya faru.
Kakakin ‘yan sandan jiihar Oyo, PPRO SP Olugbenga Fadeyi, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi.
Fadeyi ya kara da cewa; an zargi Marigayin da cewa ya kashe kansa ne ta hanyar rataya, inda kuma aka kai gawarsa asibitin Adeoyo state Hospital.
Ya zuwa hada rahotan nan bayanai ba su tabbatar da dalilansa na rataye kansa ba.