Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Bayela sun yi nasarar cafke wani babban ɗan ƙungiyar asiri bayan ya tafka mummunar ta’asa a Yenagoa, babban birnin jihar ta Bayelsa.
Ɗan ƙungiyar asirin ya shiga komar ‘yan sandannsandan bayan ya kashe wasu mutum huɗu a wata majami’a dake ƙauyen Azikoro da ke Yenagoa, a daren Laraba.
Rundunar ba ta bayanna sunansa ba amma kakakinta na jihar, SP Asinim Butswat cikin wata sanarwa a ranar Juma’a, ya ce an kama wanda ake zargi ne a ranar Alhamis, 6 ga watan Agustan 2020.
SP Butswat ya ce mutumin ya amsa laifinsa, yana kuma ba da haɗin kai har ya kai su wata mafaka inda aka gano miyagun makamai ciki har da bindiga kirar AK-47 da alburusai.
A yayin ci gaba da bincike, jami’in ya ce Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Mike Okoli, ya tura karin jami’ai domin gano sauran ’yan ƙungiyar asirin da suka tsere.
Dama wannan ɗan ƙungiyar asirin yayi shuhura wajen aikata muggan laifuka a jihar ta Bayela, kuma hukumar ‘yan sanda ta jima tana farautarsa sai a wannan karon ne tayi nasarar cafke sa.