Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki, ya bayyana cewa har yanzu akwai wasu gwamnoni daga cikin jam’iyyar APC na bashi goyon baya duk da ficewa da yayi daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar adawa ta PDP.
Kwamitin tantancewa na jam’iyyar APC dai sun ki amincewa da takardun makarantu gwamnan inda suka ce akwai lauje cikin nadi, wanda kuma suka kafa hujja da cewa shi ne dalilin da yasa suka bashi dama.
Gwamnan dai ya samu nasarar tantancewa a sabuwar jam’iyyar tasa, kuma da takardun da aki tantance a jam’iyyar ta APC.
“Na bayyana a gaban kwamitin, kuma sun tantance ni cikin daraja da karramawa, kana gani kasan an shirya komai cikin adalci, na gabatar musu da takarduna sun duba kuma ba a samu wata matsala ba, zaka iya tambayarsu don samun tabbaci” inji gwamna Obaseki.
Da aka tabo ɓangaren masu mara masa baya, gwamnan ya bayyana cewa akwai gwamnoni da dama da suke APC wanda suna goyon bayansa, sannan ya kara da cewa akwai masu sarautun gargajiya, masu kudi da manyan mutane dake sassan ƙasar duk suna goya masa baya kan takarar da yasa gaba.
Sai dai in ya yi nasarar tsayawa takarar zaɓe a inuwar jam’iyyar PDP, to dole ne yayi tafiya da tsohon ɗan takarar jam’iyyar da ya kayar a zaɓen 2016, wato Osagie Ize-Iyamu a matsayin wanda zai mara masa baya.